Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 68 Ya Ubangiji Yesu, Mun Taru Wurinka Lyrics
1
Ya Ubangiji Yesu, mun taru wurinka, Tunanin mutuwarka sun cika zukata.
Mun ji muryarka Yesu, “Gurasan nan ku ci,
Raina ne da na bayar don tunawa da ni.”
2
Ta wurin ikon Allah, kai farin haihuwa ne,
Mu kuma za mu tashi mu zauna wuri ɗaya. Alkawarinka Yesu, ƙoƙon da muka sha,
Jininka ne ya sayi rai na har abada.
3
Ƙaunarka, Mai Cetonmu, ta wuce saninmu,
Tunanin raɗaɗin da ka sha dai dominmu.
Yanzu kuwa cikin Sama addu’a ka ke yi.
Ka riƙe mu, ya Yesu, mu ƴan Ekklesiyarka. Amin