Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 67 Mai Cetonmu, Kan Giciyenka Lyrics
1
Mai Cetonmu, kan giciyenka,
Ka shaida mana ƙaunarka,
Raɗaɗinka cetonmu ne,
Jininka kuma ranmu ne.
2
Mu naka ne, Mai Fansarmu,
Da jininka ka cece mu,
Ka kwance mu da ikonka,
Har ka maishe mu ƴaƴanka.
3
Mu naka ne, Shugabanmu,
Jikinmu, ranmu, ruhunmu,
An saye mu da jininka,
Domin mu aika nufinka.
4
Gurasar rai, ciyad da mu,
Rijiyar rai, shayad da mu,
Ka ba mu ruhun yardar rai,
Ka tsarkake mu fa sosai.