Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 66 Gurasar Rai, Ciyad da Ranmu Yau Lyrics
1
Gurasar rai, ciyad da ranmu yau,
Yunwa ta ja mu zuwa gidanka.
Da dukan zuciya mu ke nemanka,
Albarkaci Maganarka yanzu.
2
Rijiyar rai, ƙishi ne mu ke ji.
Kogunan duniya duka muka ƙi.
Rijiyar rai, ƙosad da dukanmu
Koguna masu rai dai mu ke so.
3
Maganar rai, kai hasken duniya ne,
Kai mu ke bi, kai kuwa Shugaba ne,
Ka ji addu’o’inmu duka yau,
Ka bi da mu, ya Yesu, har ka zo.