Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 64 A Cikin Daren Nan da Aka Ba da Shi Lyrics
1
A cikin daren nan da aka ba da shi,
Ya sanya jibin nan na tunawa da shi.
2
“Gurasan nan,” ya ce, “Jikina ne, ku ci,
Ƙoƙon jinina ne, jinin alkawari.”
3
“Mai cin abincin nan, mai shan ƙoƙon nan kuwa,
Shelata ya ke yi, shelata mutuwata.”
4
“In ka ci namana, in ka sha jinina,
Ba za ka ji yunwa ko ƙishi ba daɗai.”
5
Ya Ubangijinmu, ƙosad da ranmu yau.
Kullum ka ciyad da mu har ranar zuwanka.