Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 63 Can Wani Tudu Bayan Gari, Ka Yanka Sadaka Lyrics
1
Can wani tudu bayan gari, ka yanka sadaka,
Ka ba da rai mai tsarki mai kawo gafara.
2
Ran Yesu ne Allah ya sa ya fanshi namu rai.
Mai isa shafe laifinmu da jininsa kaɗai.
3
Mun kasa biyan bashinmu, nan duniya ba mai biya.
Mai buɗe ƙofar rai, sai shi, Mai Ceto, Mai Shari’a.
4
Ba za mu iya kwatanta iyakar ƙauna ba.
Alhakinmu mai girma dai, ya karye zuciyarsa.
5
Ai, za mu naɗa Sarkin nan, mu shiga bautarsa.
Har zuwa iyakar duniya mu kafa mulkinsa