Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 61 Ga Littafi A Hannunka, Littafi Mai Tsarki Ne Lyrics
1
Ga littafi a hannunka, Littafi Mai Tsarki ne.
Ya fito wurin Allahnmu zuwa ga mutane.
KORUS
Zancen rai da ceto, zance na gidan gobe.
Mu karanta shi, mu bincike shi,
Littafi Mai Tsarki ne.
2
Sai mu duba littafin nan, mu bincike shi duka.
Don maganarsa gaskiya ce daga wurin Allah.
Korus
3
Sai mu haddace ayoyi, mu ƃoye su a zuciya
Don su hana mu zunubi, su gyarta halinmu.
Korus
