Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 606 Ƴanuwa, Ku Zo Mu Bi Yesu Lyrics
Ƴanuwa, ku zo mu bi Yesu
Ƴanuwa, ku zo mu bi Yesu
Yesu ne ya zama cetonmu.
Ƴanuwa ku bar ɗinkin laya
Laya ba ya iya cece mu
Yesu ne ya zama cetonmu
Yesu ne ya zama cetonmu.
Ƴanuwa ku bar ɗinkin guru
Guru ba ya iya cece mu.
Yesu ne ya zama cetonmu
Yesu ne ya zama cetonmu.
Ƴanuwa ku bar tsaka tsaka
Ƴanuwa ku bar tsaka tsaka
Ran da mutuwa ta zo, ta ɗauke ka.
A kira masu bi su zo su bizne ka
Su zo su ƙi, su ce ba ka addininsa.
Sa’annan kana tsaka tsaka.
A bizne ka babu yin addu’a,
Ga Littafi Mai Tsarki ya shaida mu a nan
Abin da aka ɗamre anan a duniya
A ɗamre shi ya zama can samaniya
Ƴanuwa ku bar tsaka tsaka
Yesu ne ya zama cetonmu.