Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 605 Ƴan’uwa Ƙarshenmu Kenan Fa Lyrics
1
Ƴan’uwa ƙarshenmu kenan fa.
Ƴan’uwa mu guje ma fushinsa
Sa’anda mai ceto za ya komo.
Mai zunubi za ya ji tsoro,
KORUS
Ji tsoro, ji tsoro,
ku tudai, ku tudai
girgiza, girgiza kan teku,
itatuwa ku nemi mafaƙa dukan duniya.
Mai ceto ya zo.
2
Allah fa zai fito daga sama
Tare da dukan, mayakansa.
Dukan kabilu fa za su taru
kewaye da mazamninsa can.
Korus
3
Za mu hau sama, mu tarƃe shi
tare da murna ba iyaka.
Akwai bakinciki ga waɗanda
ba za su tarƃe shi da murna.
Korus
4
Ƴan’uwa ji ku karƃa ku rayu
kamin ranar shari’a ta zo.
Allah yana zuwa da ladansa.
zai raba bisa ga aikinmu.
Korus
