Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 60 Maganar Allahnmu Fitila Ce Lyrics
1
Maganar Allahnmu fitila ce,
Ta ba da haskenta bisa hanyarmu.
Ta nuna hanyarmu da za mu bi sosai.
Ta nuna mugunta, mu yi gudunta.
2
Maganar Allahnmu wuta ce fa.
Tana ƙone mugunta, da ƙazanta duk.
I, ta kan tsarkake zuciyar Masu Bi,
Haske ya shiga kuwa da murna sosai.
3
Maganar Allahnmu takobi ne,
Allah ya ba mu shi, mu sari maƙiyi.
Shaiɗan zai ji tsoron mai riƙon takobin.
Mun iya kwaƃe shi da maganan nan.
4
Ya ku ƴanuwana, mu yi aniya,
Tsarkake zuciya da maganarsa.
Domin mu ƙarfafa, kullum mu karanta
Littafi Mai Tsarki, ƙyautar Allahnmu