Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 6 Mu Yi Sujada Ga Ubangiji Lyrics
1
Mu yi sujada ga Ubangiji,
Mu yi godiya domin ƙaunarsa.
Da zuciya ɗaya mu ɗaukaka shi,
Mu yabi sunansa da duk ladabi.
2
Mu yi tunani a kan girmansa,
Mu yi waƙoƙi kan alherinsa,
Mai Tsarki, Mai Ƙauna, Mai Gaskiya ne,
Mai ikon halitta, mai jin addu’a.
3
Bukatarmu duk shi ya ke ta biya,
Mu karƃe su fa tare da godiya.
Abinci, abin sha, numfashi da rai,
Lissafin kyautansa ya fi ƙarfinmu.
4
Mu raunana ne, amma cetattu,
Mu ƴaƴansa ne, bai yashe mu ba.
Yana marmari dai mu yi zumunta,
Jiƙansa mai yawa, ba misalinsa.
5
Al’amuranmu su girmama shi,
Da bakunanmu mu yi ta shaida.
Mu bauta masa, mu ji tsoronsa kuwa,
Gama shi ne Allah na duk duniya.
