Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 592 Zamanin da Almasihu Ɗan Allah Lyrics
Zamanin da Almasihu Ɗan Allah
Ya ji tausayinmu mu ɓatattu,
Shi ma ya rabu da gida Ubansa
Sa’annan ya zo zaman tare da mu.
KORUS
Zuwan Mai Ceto ƙamna ta sa shi
Allah ya ba shi don duniya duk
Kada su halaka, sai dai su sami
Ainihin rai irin nasa sosai.
2
Zaman Mai Ceto a cikin mutane
Da yawan so da alheri ya ke
Kowa ya nema ya gamu da Yesu
Sani ya yi shi Mai Taimako ne.
KORUS
3
Zaman nan nasa na bada alheri
Aibunsa babu, bin Allah ya yi
Ransa ya bayar don fansar mutane,
Allah ya karɓa. Tsattsarka ne shi.
Korus
4
Domin zunubinmu Yesu ya mutu,
Bayan ya mutu ma sai biznewa
Shi ma ya tashi a rana ta uku
Sa’anna ya hau sama wurin Uban.
Korus
5
Yesu Mai Cetonmu zai sake zuwa
Daidai alkawali wanda ya yi
Sa zuciyarmu dai kowace rana
Yesu mu gan shi, mu gamu, mu ji.
Korus