Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 59 Mun Gode Maka, Allahnmu Lyrics
1
Mun gode maka, Allahnmu,
Domin maganar gaskiyarka,
Umarninta ne haskenmu,
Koyarwarta fitila ce.
2
Maganarka mai tsarki ce,
Mun kafa bege cikinta,
Maganarka duk gaskiya ce,
Bari ta zauna a zuciyata.
3
Maganarka ce takobi,
Takobi kuwa na Ruhunka,
Ka sa ta soki zuciyarmu,
Ta tsautar, har ma ta kwaƃe mu.
4
Ya Allah, buɗe zuciyarmu,
Haskaka kuma duhunmu,
Ka buɗe kuwa fahiminmu,
Ka koya mana, Allahnmu.