Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 589 Zaɓaɓɓe Na Allah, Shi Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 589 Zaɓaɓɓe Na Allah, Shi Lyrics

 

1
Zaɓaɓɓe na Allah, shi
Aikkake na ainihi
Nufin Allah duk yayi,
Ubangiji, Almasihu.

2
Yesu aka kunyata
“Shi ba wani abu ba,”
Aka ce. Ai, shi ya sa
Aka raina Almasihu.

3
Shi a jikin gungume
Ga shi nan kwa, ɗaurarre!
Aka kashe shi sosai,
Mai Alheri ne ya mutu.

4
Mutumcinsa aka ci,
Zub da jini aka yi,
Karɓar ceto aka ƙi,
Jinin Yesu ya panshe mu.

5
Riƙe shi ba dama fa
Ko a wurin mutuwa,
Allah ma ya ɗaukaka
Ɗansa, Yesu Almasihu.

6
In ya komo wata rana,
Zai tashe mu daga nan.
Har ya kai mu gun Uban,
Rerawa mu yi ma Yesu.

Exit mobile version