Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 587 Yunana Lyrics
YUNANA
1
Ubangiji ya yi magana da Yunana
Ya ce “Yunana ka tashi ka je Nineva
Ka shaida masu bishara domin su tuba
Gama muguntarsu ta hau zuwa gareni.”
KORUS
Mu masu bi yau, mu yi biyayya
Ga magana Ubangiji
Ubangiji fa ba mutum ba ne
Don haka mu yi biyayya da maganarsa.
2
Amma Yunana ya tashi domin ya gudu
Daga fuskar Ubangiji zuwa can Tarshish
Ya gangara zuwa Yafa ya shiga jirgi
Yana murna wai ya gudu a fuskar Allah.
Korus
3
Yunana ya manta Allah yana ganinsa
Sai Allah ya nuna Ikonsa ga Yunana
Ya aiko babban iska da haɗari
Sai Yunana ya tuna Allah yana ganinsa.
Korus
4
Allah ya shirya babban kifi cikin teku
Kifi ya haɗiye Yunana har kwana uku
Nan da nan Yunana ya tuna akwai Allah
Wane ne zai gudu daga fuskar Ubangiji.
Korus
5
Cikin duniya yau akwai irin Yunana
Waɗanda ba su so su bi Ubangiji ba
Suna ruɗin kansu cewa za su guje shi
Suna manta Allah ne mahalicin duniya.
Korus