Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 586 Yesu, Ɗan Allah, Mai Iko Duka Ne Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 586 Yesu, Ɗan Allah, Mai Iko Duka Ne Lyrics

 

(Kira da Amsa

K : Yesu, Ɗan Allah, Mai Iko duka ne,
A : Yesu shi sarki ne, Sarkin Sarakuna.

K : Ya bar sarauta a can cikin sama,
A: Ya zo a duniya a cikin talauci,

K: Ya sha wahala a gun Yahudawa
A: Har suka yi shawara, suka giciye shi.

K: Ya yi mutuwa fa, mutuwa ta giciye,
A: Ya zubda jinisa domina ya panshe mu.

K: Bayan kwana uku sai Yesu ya tashi.
A: Yesu ya ci nasara, nasara ta mutuwa.

K : Ku fa mutane, ku zo fa mu tuba,
A : Mu bi Yesu Mai Nasara da mutuwa.

K : Sai fa, mu bi Shi da zuciya ɗaya
A : Gama babu ceto sai wurin Yesu fa.

K: Ku zo maza mutane ku zo maza mu tuba
A: Yesu ya hau sama yana shirya wuri.

K: Za ya sake zuwa domin masu-binsa.
A: Lalle akwai murna ran da mun kai sama.

K: Yesu mun gode domin mutuwarka.
A: Yesu mun gode domin kai, ka tashi.

K: Karɓi sarauta da iko da girma.
A: Taka ce har abada, har abada abadin.

Exit mobile version