Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 584 Yesu Ya Mutu A Kan Giciye Lyrics
1
Yesu ya mutu a kan giciye,
An saukar da jikinsa.
Aka baiwa uwarsa Maryamu
Ta yi baƙin ciki.
(Solo – ya kira
KORUS
Da murya mai ƙarfi ya ce,
“Eli, Eli, lama sabactāni ?
Wato ya Allah, ya Allahna,
Don mi ka yashe ni ? ”
2
Almajirai suka dauki Yesu
Da iznen Romawa daga hannun uwarsa
Suka sa shi a cikin Kabari
Suka rufe ƙofa.
Korus
3
Yesu ya mutu a ran juma’a.
An bizne shi a ran nan.
Yesu ya tashi a ran Lahadi,
Wato ran Paska ke nan.
Korus
