Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 583 Yesu Ya Ci Nassara da Mutuwa Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 583 Yesu Ya Ci Nassara da Mutuwa Lyrics

 

KORUS
Yesu Almasihu ta wurin mutuwarsa
Ya ci nassara da mutuwa
Ya ba mu iko mu masu bi
Nasara bisa magabci

1
Ranar mutuwar Yesu Kristi kan giciye
Shaiɗan da mutanensa ke murna
Amma dukan masu binsa
Su ne ke nuna baƙin ciki.
Korus

2
Amma ranar tashin Yesu Kristi daga Kabari
Dukan masu binsa ke murna
Amma Shaiɗan da masu binsa
Su ne ke nuna baƙin ciki.
Korus

3
Babban kuskuren da Shaiɗan ya yi a tarihinsa
Shi ne giciye Almasihu
Amma bai sani ba ya kada kansa
Amma bai sani ba ya murɗe kansa.
Korus

Exit mobile version