Skip to content

info@example.com

Treasure Hymns – Hausa

  • Home
  • Littafin Wakoki Hausa Hymns
  • Sample Page
  • Home
  • Littafin Wakoki Hausa Hymns
  • Sample Page

Hymn 58 Yanzu, Ya Uba, Muna Tunawa Lyrics

  1. Home   »  
  2. Hymn 58 Yanzu, Ya Uba, Muna Tunawa Lyrics

Hymn 58 Yanzu, Ya Uba, Muna Tunawa Lyrics

January 10, 2026 treasurehymnsLittafin Wakoki Hausa Hymns

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 58 Yanzu, Ya Uba, Muna Tunawa Lyrics

 

1
Yanzu, ya Uba, muna tunawa
Da ƙaunarka mai kawo fansarmu.
Sabili da jinƙanka mai yawa,
Mun zo ta wurin Matsakancinmu,
Wanda ya ba da kansa dominmu
Domin ya fanshi dukan zukata.

2
Ya Uba, duba fuskar Almasihu,
Ka sa a iske mu a cikinsa .
Kada ka duba kasawarmu dai,
Mu masu ƙanƙantar bangaskiya.
Gama shaidar cetonmu mu ke yi
Daga laifofinmu da hakkinsu.

3
Ka ji addu’armu da za mu yi
Sabili da masoya, ƴanuwa,
Ka kare su dai daga hatsari,
Ka kiyaye su cikin lafiya
Ka ba su nasara a duniya,
Su zama naka fa har abada.

4
Mu ma mun zo mu amsa kiranka,
Ya Yesu mai ƙauna ba iyaka.
Ta wurin jinƙanka da jininka,
Ka cece mu duk daga mugunta.
Ka karƃe mu mu zama bayinka,
Ka sa mu zauna kullum cikinka.

Post navigation

Previous: Hymn 565 Yesu Babban Mai Magani Lyrics
Next: Hymn 556 Yabo Guda Ɗaya Cikin Waƙarmu Lyrics

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent Posts

  • Hymn 346 A Cikin Farko Allah Ya Halitta Sama da Ƙasa Lyrics
  • Hymn 215 A Cikin Duniyan Nan Yanzu Lyrics
  • Hymn 218 A Cikin Dukan Halin da Mu Ke, da Murna Da Wahala Lyrics
  • Hymn 64 A Cikin Daren Nan da Aka Ba da Shi Lyrics
  • Hymn 347 A Cikin Farko Allahnmu Lyrics

Recent Comments

  1. A WordPress Commenter on Hello world!

Archives

  • January 2026

Categories

  • Littafin Wakoki Hausa Hymns
  • Uncategorized
Proudly powered by WordPress | Theme: goldy-mex by inverstheme.
Go to mobile version