Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 575 Yesu Mai Ceto, Lalle Shi Ne Mai Cetonmu Lyrics
Yesu Mai Ceto, lalle shi ne mai cetonmu
Muna murna murna mai yawa za mu yi,
Domin Yesu ya mutu domin laifinmu.
Ya mutane. ku tuba, ku tuba,
Ku tuba, ku bi Yesu.
Kada ku zamna a cikin zunubanku.
Ku zo yanzu, ku tuba, ku bi Yesu.
Ba wata hanya do za mu sami ceto
Ba wani Allah a cikin wannan duniya,
Da ya iya ya wanke zunubanmu.
Sai Yesu kaɗai, Ɗan Allah mai iko duka,
Shi ne ya zo, ya mutu domin laifinmu
Shi mai rai ne, ya tashi, ya tashi,
Ya tashi daga kabari.
Ya hau sama, yana shirya mana wuri.
Wata rana za mu je, za mu je,
Za mu je gidan Allah.
Za mu raira waƙoƙi na yabonsa
Mu ce masa, halleluya, halleluya,
Za mu ce masa, halleluya, Amin.