Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 573 Yesu Kristi Yana Zuwa Don Ya Ɗauki Masu Bi Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 573 Yesu Kristi Yana Zuwa Don Ya Ɗauki Masu Bi Lyrics

 

1
Yesu Kristi yana zuwa don ya ɗauki masu bi
Bar mu kasance da shiri, fitilinmu suna ci
Wanda ya yi shiri duka zai tafi tare da shi
Yesu yana dawowa a duniya.

KORUS
Yesu yana dawowa a duniyan nan
Don ya fyauci masu bi, Ya kai su can.
Ka yi shiri fa mai bi, ka daidaita tafiyarka,
Yesu yana dawowa a duniya.

2
Duba ango yana zuwa, ba labari, ba zato
Ranan nan ba sauran tuba, ba kuwa wani taimako.
Kada dai ka yi jinkiri har Ubangiji ya zo.
Yesu yana dawowa a duniya.
Korus

3
Wanda ba ya karɓi Yesu ba zai shiga damuwa,
Babu sauran shirin kome, babu sauran gafara.
Kai da ka ke ƙin Mai Ceto, rabonka sai balaka
Yesu yana dawowa a duniya.
Korus

4
Can a sama Gidan Allah, yawan daɗi za mu ji
Muna nan tare da Yesu, muna hutawa da shi
Babu sauran ɓacin zuciya, babu sauran a zunubi
Yesu yana dawowa a duniya.
Korus

Exit mobile version