Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 570 Yesu Kristi Mu Ne Naka Lyrics
1
Yesu Kristi mu ne naka
Za mu bi ka ko’ina
Za mu tada tutar namu
Za mu bi maganarka
Mu ƴan yaƙin ka, ya Yesu
Za mu bi ka ko’ina. [2x]
2
Cikin duhun wannan duniya
Za mu nuna haskenka
Za mu keɓe zukatanmu
Daga dukan zunubi.
Mu ƴan yaƙinka, ya Yesu
[Za mu bi ka ko’ina.] 2x
3
Ubangiji muna roƙo
Tsarkakke ƴan yaƙinka
Ban da za ka dawo nan kuwa
Iske mu da aminci
Mu ƴan yaƙinka, ya Yesu
[Daga nan har abada.] (2x
