Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 57 Ya Allahnmu Madauwami Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 57 Ya Allahnmu Madauwami Lyrics

 

1
Ya Allahnmu Madauwami,
Kai ne ka halicci teku,
Da koguna da taffukan
Da su ke cikin duniya.
Ka ji mu don ƴanuwanmu,
Da jinƙanka ka dube su.

2
Ka tsare su da ikonka.
Idan hadari ya taso,
Ko iska ce mai fyaucewa
Ta girgiza jiragensu.
Ka ji mu, muna roƙonka,
Su kai kwata ma lafiya.

3
Mun tuna yadda Almasihu,
Ya shiga cikin jirgi da.
Ya tsauta wa raƙuman ruwa,
Sun kwanta, sun natsu sosai.
Ka ji yanzu, ya Almasihu,
Ka tsare ƴanuwanmu yau.

4
Ka tsame su da ikonka
Daga masifu masu yawa,
Su dogara gare ka kuwa,
Su sansance amincinka.
Dukanmu za mu yabe ka,
Ya Allahnmu mai ta’aziyya.

Exit mobile version