Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 569 Yesu Ina Yabonka Lyrics
KORUS
Yesu ina yabonka domin kai ka cece ni
Ina cike da murna don wannan alherinka
Har ka bada jininka (fansata ni mai zunubi
1
Alherin mai cetona yana da daɗin ji
Ya cece ni da jininsa (don yana ƙaunata
Korus
2
Da can fa ni batace ne, Yesu Kristi ya same ni
Da can fa ni makoho ne (ya buɗe idanuna
.
Korus
3
Ubangiji ni zan bayar domin wannan alherinka
Zan miƙa jiki haɗaya (tare da zuciya
Korus
4
Ruhun alheri zugani, ƙarfafa niyata
Ka bishe ni cikin waƙa (In shaida bishararka
Korus