Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 567 Yesu Gaban Kayafas Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 567 Yesu Gaban Kayafas Lyrics

 

1
Yesu gaban Kayafas, Yesu gaban mayan malamai,
Yesu gaban Bilatus, domin ya fanshe ni.
An yi masa bulala, an yi masa ba’a,
Yesu ya sha wahala, domin ya cece ni.

KORUS
Yesu ya sha wahala (3x

Domin ya fanshe ni.

2
An tofa masa miyau, da babbakun magana.
Yesu ya ɗauki giciye domin ya fanshe ni.
Yesu a bisa giciye, ya zub-da jininsa,
Yesu a cikin Kabari, domin ya cece ni.
Korus

3
Yesun mu ya tashi da rai,
Yesun mu yana da rai
Yesu ya hau cikin sama
Domin mu sami rai

4
Ka tuna domin ran dawowarsa
Gama ranar nan ƙarshe ne. Bass : “Ƙarshe ne”
Ƙarshe ne, ƙarshe ne,
Gama ranan na ƙarshe ne.
Korus

5
Ka tuna da miyagun ayyukanka daina su
Kamin Yesu ya dawo. Bass:”A ƙarshe
Ayyukan miyagu, ka daina su
Kamin Yesu ya dawo.
Korus

6
Ka tuna randa za ka Kabari
Gama ranan nan ƙarshe ne.
Ƙarshe ne, ƙarshe ne
Ran da za ka Kabari, ƙarshe ne.
Korus

Exit mobile version