Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 564 Yesu Ba Shi da Hannu Sai Namu Lyrics
1
Yesu ba shi da hannu sai namu
Don aikinsa nan duniya
Ba shi da ƙafa sai namu
Don a biɗa masu ɓacewa.
Ba shi da harshe sai namu
Don a shaida mutuwar Yesu
Ba wata hanya sai ranmu
Don a furta bisharar ceto.
2
Duniya ba ta san karatu
Mu ne littafinsu nan.
Masu zunubi na diban mu
Ko mu masu-gaskiya ne.
Aikinmu maganarmu duka
Su ne labarin Yesu.
Ko duniya ta ga Mai Cetonka.
Ko sun rasa, ganinsa yau?
3
Ina labarin na aikinka yau?
Ko nashi ko naka ka yi?
Ina ƙafa ta kai ka yau ?
Ta bi duniya ko Ubangiji ?
Ina magana da ka faɗi yau ?
Ko Yesu ya faɗi ko kai ?
Ko zuwa na Yesu ya fi kusa yau
Sabo da ka shaidarshi.