Skip to content

info@example.com

Treasure Hymns – Hausa

  • Home
  • Littafin Wakoki Hausa Hymns
  • Sample Page
  • Home
  • Littafin Wakoki Hausa Hymns
  • Sample Page

Hymn 562 Yau Cikin Birnin Dauda An Haifa Mana Mai Ceto Lyrics

  1. Home   »  
  2. Hymn 562 Yau Cikin Birnin Dauda An Haifa Mana Mai Ceto Lyrics

Hymn 562 Yau Cikin Birnin Dauda An Haifa Mana Mai Ceto Lyrics

January 10, 2026 treasurehymnsLittafin Wakoki Hausa Hymns

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 562 Yau Cikin Birnin Dauda An Haifa Mana Mai Ceto Lyrics

 

1
Yau cikin Birnin Dauda an haifa mana Mai Ceto.
Yau Yesu ya shigo duniya, Ɗan Allah mai girma.
Cikin sakarkari an kwantadda shi.
Shanu suna kallonsa, ana yabon mai girma.
A can a Baitalahmi an haifi Kiristi
Shi ne, shi ne maɗaukaki, Allah mai girma.

2
Mala’ika fa yau ya zo gun makiyaya.
Ya ce masu, Yau Kiristi Ɗan Allah ya iso.
Annabawa sun yi annabcin zuwansa.
Annabcinsu ya fi saninmu, Ɗan Allah ya iso.
Mu je mu gaida jaririn nan mai ceto.
Shi ne, shi ne, ɗan ragon Allah mai ceto.

3
Yau mala’iku cikin sama suna ta yabo.
Suna cewa Alhamdu ga AIIah a duni ya salama.
Babban Sarki ne a duniyan nan duka.
Ɗaukaka duka nasa ne, an haifa mana mai ceto.
Halle-Halleluya Ɗan Allah, sabko.
Yau ne an haifi wannan sarkin Yahudawa.

4
Shehuna sun ga tamraron nan daga gabas.
Yanzu a Baitalahmi sun ga tamraron nan,
Sun zo sun durƙusa, suna ta yabo,
Kayan zinariya ne suna zuba gun Yesu.
Mu je mu kawo ziyaramu gun Yesu,
Mu je, mu yabi jaririn nan mai ceto.

5
Halleluya. Halleluya, Kiristi ya iso
Aikakke ne shi, tilo ‘Dan Allah ya iso.
Yahudawa suna ta jiran zuwansa.
Har wa yau ba su sani yau ne Kiristi ya sabko
Har yau suna ta jiran Kiristi mai ceto,
Har yau suna ta duban hanyar mai ceto.

Post navigation

Previous: Hymn 565 Yesu Babban Mai Magani Lyrics
Next: Hymn 556 Yabo Guda Ɗaya Cikin Waƙarmu Lyrics

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent Posts

  • Hymn 346 A Cikin Farko Allah Ya Halitta Sama da Ƙasa Lyrics
  • Hymn 215 A Cikin Duniyan Nan Yanzu Lyrics
  • Hymn 218 A Cikin Dukan Halin da Mu Ke, da Murna Da Wahala Lyrics
  • Hymn 64 A Cikin Daren Nan da Aka Ba da Shi Lyrics
  • Hymn 347 A Cikin Farko Allahnmu Lyrics

Recent Comments

  1. A WordPress Commenter on Hello world!

Archives

  • January 2026

Categories

  • Littafin Wakoki Hausa Hymns
  • Uncategorized
Proudly powered by WordPress | Theme: goldy-mex by inverstheme.
Go to mobile version