Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 56 Ya Ubanmu Na Cikin Sama Lyrics
1
Ya Ubanmu na cikin Sama,
Dubi abokanmu,
Sa musu duka albarkarka,
Ka daɗa murnarsu.
2
Ka yafe musu laifofinsu,
Ba su salamarka,
Cece su daga wahalarsu,
Ta wurin ikonka.
3
Ka gyara musu tunaninsu,
Ka tsare harshensu,
Tsabtad da dukan zukatansu,
Cika ruhohinsu.
4
Daga makidai na Iblis,
Daga duk ruɗewa,
Bisa kowane kumamanci,
Ka ba su nasara.
5
Kuma bari su gaskata fa
A hannunka su ke.
Bishe su kullum da ƙaunarka,
Gama su naka ne.