Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 556 Yabo Guda Ɗaya Cikin Waƙarmu Lyrics
Yabo guda ɗaya cikin waƙarmu,
Haske za mu bayar domin waɗansu
Sai mu badar shaidar Yesu fa yanzu
Bi shi, bi shi, za ni bi Yesu
In ɗaya ce zan je domin shaidarsa.
Tashi, tashi, kama aikin Yesu.
Mu masu bin Yesu mu yi ta yi.
Akwai hanyoyi guda biyu ne
Babbar ta nufa wajen hallaka
Hanyar ƙaramar ta nufa wagen hallaka
Kai ne da zaɓen wanda za ka bi.
Zaɓi hanyar wanda za ka bi yau,
Ko babbar ko ƙaramar,
Zaɓi mafi kyau
Ni na zaɓi ƙanƙanuwar hanyar
Domin in sami rai na har abada.
