Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 552 Ya Yesu Mun Kangara Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 552 Ya Yesu Mun Kangara Lyrics

 

1
Ya Yesu mun kangara,
Gagara muka yi,
Tun muna ƙanƙanana
Zamanmu zaman ƙi.
Shaiɗan ya magance mu
Ya raba mu da kai
Da muka yardar masa
Ya ɓad da mu sosai.

2
Ya Yesu, muguntarmu
Yanzu sai daɗuwa
Kamar ta halaka mu
Mu ma, har abada
Mun yiwo gudun tsira,
Da roƙo, muka zo
Da ƙazantaccen ranmu
Ka wanke shi ƙalau.

3
Sa’annan, ya Ubangiji
Mu naka sababbi,
Ka tsare mu ga Mugun,
Har bi da mu ka yi.
A kwananmu a gaba
A hannunka mu ke
Biyayya har ta kasa
Ga mu, mu naka ne.

Exit mobile version