Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 55 Ya Uba Na Cikin Sama Lyrics
1
Ya Uba na cikin Sama,
Sunanka mai tsarki ne,
Mulkinka shi zo, ya AlIah,
Yadda ka ke marmari.
2
Duk abin da ka ke nufi
Sai mu aikata a nan,
Kamar yadda a ke yinsa
Cikin gidanka a can.
3
Ba mu yau abincin yini,
Bisa ga alherinka.
Alhini ba za mu yi ba,
Sai mu yi bangaskiya.
4
Gafarta kurakuranmu,
Na junanmu za mu yi.
Daga jaraba da mugu,
Tsare mu, Mai Cetonmu.
5
Girma, iko, duk da mulki
Naka ne har abada.
Cikin sunan Almasihu
Muna roƙonka. Amin.