Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 547 Ya Allahna Lyrics
1
Ya Allahna ina ta yin mamaki
Kan ayyukan waɗanda kai ka yi
Ka hallici sammai da dukan duniya
Kana ta mulkin su ba fasawa.
KORUS
Sai dai in shaida daga zuciya
Babu misalin girmanka.
2
Ka yi magana da tekuna sun taru
Ka sa ta tsiro da anfaninta
Ka hallici ɗan Adam cikin duniya
Ka ba mutum lumfashin hancinsa.
Korus
3
Amma abin da ya fi ban mamaki
Shi ne yadda ka ba mu mai fansa
Ɗanka ya zo ya mutu maimakonmu
Cikin wannan mugunwar duniya.
Korus
4
Ran da zan tsaya gaban kursiyinka
Zan ga dukan ɗaukakar ka
Zan tuna yadda cikin yawan ƙaunar
Ka ba mu salamar ka
Korus