Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 542 Wannan Duniya Babu Salama Fa Lyrics
1
Wannan duniya babu salama fa.
Mutane suna neman salama
ta wurin neman kayan duniyan nan.
Komi ka samu a can zai dawama.
KORUS
Nemi Yesu tun yanzu ƴan’uwa, ɗan’uwa,
gidan Yesu da cikakken salama,
a can sama ba kamar duniya ba.
Komi ka samu a can zai dawama.
2
Wannan duniya babu salama fa.
Dubi masu arzikin duniya nan,
sun gina gidaje masu daraja.
Duk da haka ba su da sakewa can.
Korus
3
Wannan duniya babu salama fa,
dubi masu ilimin duniya nan,
Suna da jirage da motoci.
Duk da haka wasu na Kisan Ƙansu.
Korus
