Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 541 Wanene Shi Ɗan Maryamu Lyrics
1
Wanene shi Ɗan Maryamu
Ta haifi ɗa wurin Ruhu ?
Shi ne Yesu Ɗan Allah,
Shi ne Yesu Mai Cetonmu.
Sai mu faɗi gabansa,
Mu naɗa shi Ubangiji.
2
Wanene shi da ya mutu,
Sabili da zunubanmu ?
Shi ne Yesu Ɗan Allah,
Shi ne Mai Cetonmu.
Sai mu faɗi gabansa
Mu naɗa shi Ubangiji.
3
Wanene shi ran Lahadi
Ya fito daga kabari?
Shi ne Yesu Ɗan Allah,
Shi ne Yesu Mai Cetonmu,
Sai mu faɗi gabansa
Mu naɗa shi Ubangiji.
