Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 536 Walƙiya, Walƙiya, Tamrari Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 536 Walƙiya, Walƙiya, Tamrari Lyrics

 

1
Walƙiya, walƙiya, tamrari
Ga su abin mamaki
Allah mai hikima ne
Shi ya sa su can lalle

Shi ya ba mu Yesu fa
Shi ya kawo gafara
Shi ya sha wahala ma
Don Shi kawo ceto fa.

2
Lokacinda Allah fa
Ya zo nan a duniya
An haife shi ɗan yaro
An sa sabon tamraro

Tamraro ya bi da su
Mai Iko ya tsare su
Har sun ga Mai Cetonsu
Suka ba shi zuciyarsu.

3
Walƙiya, walƙiya, tamraro
Bi da mu har Mai Ceto
Za mu ba shi zuicyarmu
Za mu ba shi ranmu duk

Za shi zama sarkinmu
Za shi mulk zuciyarmu.
Walƙiya, walƙiya, tamraro
Bi da mu har Mai Ceto.

Exit mobile version