Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 532 Wa Ke Samun Albarka Daga Ubangiji? Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 532 Wa Ke Samun Albarka Daga Ubangiji? Lyrics

 

1
Wa ke samun albarka daga Ubangiji ?
Wanda ya ke karanta
Daga Litaffinsa.
Har ya ji ya kiyaye
Abin da ke ciki,
Shi zai sami albarka
Daga hannuwansa.

2
Wa ke samu albarka daga Ubangiji ?
Wanda an gafarta
Masa duk laifofinsa
Ba lissafta gare
Dukan muguntarsa.
Allah zaya zubda su
Cikin zurfin teku.

3
Wa ke samu alabarka daga Ubangiji ?
Wanda ba ya biba ta
Shawarar mugu ba.
Ko a cikin hanyarsa
Ba ya tsaya a ciki,
Marmari da tunani
Cikin shari’arsa.

4
Wa ke samu albarka daga Ubangiji ?
Shi mai faɗin gaskiya
Cikin zuciyarsa.
Yana tafiya sosai
Da aikin adalci
Ba shi tsegume daɗai
Ko zagin abokan shi.

5
Wa ke samu albarka daga Ubangiji ?
Wanda a ke tsananta
Sabo da adalci
Ko mu kan sha wahala
Sabo da sunansa
Ladarmu mai girma ce
Can a cikin sama.

6
Wa ke samu albarka daga Ubangiji ?
Wanda ya ke jimrewa
Lokacin jaraba
Allah Mai aminci ne
Ya yi hanya tsira
Farin ciki mu ke yi
Don ya ci nasara.

7
Wa ke samu albarka daga Ubangiji?
Wanda ya ke jiransa
Komowar ɗan Allah.
Ya yi shirin zamansa,
Ya bar bin duniya.
Yesu yana zuwa kuwa
Biɗan masu-binsa.

Exit mobile version