Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 529 Ubangijimu Mai Yawan Ƙamna Lyrics
1
Ubangijimu mai yawan ƙamna
Wanda ya sabko domin pansarmu
Yana kira da murya mai ƙarfi
Karɓi ceto yanzu.
KORUS
Karɓi ceto yanzu, yanzu
Karɓi ceto yanzu, yanzu
Ko kana cin alwashi na gobe
Gobe ba naka ba.
2
Yana neman mu da so da yarda
Idan ka kyale za ka ƙone kwa
Yesu kaɗai ne Mai Ceton duniya
Karɓi ceto yanzu.
Korus
3
Adini ba za ya cece ka ba,
Kuɗinka ba za ya cece ka ba
Yesu kaɗai ne Mai Ceton duniya
Karɓi ceto yanzu.
Korus
4
Ƴan duniya, ku falka daga barci
Ku karɓi Mai Cetonmu tun yanzu
Za ya ba kiu rai na har abada
Karɓi ceto yabnzu.
Korus
