Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 528 Ubangiji, Makiyayi Na Ne Lyrics
UBANGIJI MAKIYAYI NA NE
KORUS
Ubangiji, ma-kiyayina
Ba zan taɓa, rasa komi.
1
Yana sanya ni, in kwanta
A cikin makiyaya mai ƙyau.
Yana bishe ni, a gefen
Ruwaye, na hutawa.
Korus
2
Hakika, ko tafiya nake yi
Ta tsaki-yar kwarin mutuwa.
Ba zan ji tsoron, masifa ba
Gama kana, tare da ni.
Korus
3
Nagarta kuma, da jinƙai
Za su bi ni duk kwanakina.
Zan zauna kuma, a gidan
Ubangiji, har abada.
Korus