Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 526 Ubangiji Shina Ta Biɗa Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 526 Ubangiji Shina Ta Biɗa Lyrics

 

1
Ubangiji shina ta biɗa
Girbi cikin ran masu bi
Shina son ɗiyan Ruhu Mai Tsarki
Da aiki na ɗaukaka shi.

KORUS
Babu kome sai da kunnuwa
Mu ba shi baƙin ciki
Maimakon ɗiyan Ruhu Mai Tsarki
Mun miƙa mai kummuwa.

2
Ko mutane suna ta gani
Ҡamnarsa cikin ranmu yau ?
Da anniya domin masu duhu
Su tuba su bada gaskiya ?
Korus

3
Ko kai za ka yarda ka zama
Littafi Mai Tsarkinsu ?
Ba su iya karanta don kansu
Sai duban zaman masu bi.

4
I, Ubangiji, na yarda
Na ba ka duk raina yau
Maimakon kunnuwa fa zan ba ka
Ɗiyan Ruhu da naka taimako.

Exit mobile version