Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 524 Ubangiji Ke Mulki Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 524 Ubangiji Ke Mulki Lyrics

 

KORUS
Ubangiji ke mulki cikin mutanensa
Wanda ke gaba da su zai rasa ɗan farinsa.
Ubangiji na cikin mutanensa
Wanda ke gaba da su zai mutu.

1
Ku tambayi Firauna ku ji, Ku tambayi Massarawa
Ina ƴaƴansa suke, ƴaƴansa na fari?
Sun taɓa mutanen Ubangiji
Sun rasa ƴaƴansu na fari.
Korus

2
Ina Firauna yake, ina mayakensa?
Ina Firauna yake, ina karusansa?
Sun taɓa mutanen Ubangiji
Sun rasa rayukansu.
Korus

3
Ku tambayi shawulu ku ji, za ku ji labari.
Ina Shawulu yake, za ku ji labara.
Ya taɓa mutanen Ubangiji
Ya rasa idanunsa.
Korus

4
Mu ne ƴaƴan Ubangiji, mu ne mutanensa.
Mu ne dangin Yesu Kristi, mu ne idanunsa.
Kowa ya taɓa ƴaƴan Ubangiji.
Zai gamu da fushin Ubangiji.
Korus

Exit mobile version