Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 52 Maƃulƃula Na Ruwan Rai, Kishi Zai Kashe Ni Lyrics
1
Maƃulƃula na ruwan rai, Kishi zai kashe ni,
Zubo da ruwan daɗinka domin ka rayad da ni.
2
Raina ya zama busasshe, ƙarfi ya gaza ma,
Ka shayad da ni da ruwanka, ya Allah, Ubana.
3
Maƃulƃula na Allahna, daga kursiyi ka zo,
Ka ƃullo cikin zuciyata, in ka yarda yanzu.
4
Kai ne mai ikon warkarwa, kai ne mai ba da rai,
Salama da alherinka su na ke so ƙwarai.
5
Ka ba ni irin ruwan nan wanda zai ƃulƃula
A cikin zuciyata sosai, rai na har abada.
