Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 519 Taruwa, Taruwa, Taruwa Gidan Allah Lyrics
Taruwa, taruwa. taruwa gidan Allah.
Godiya, godiya, godiya gidan Allah.
Akwai murna, murna, akwai murna gidan Allah.
Babu mutuwa, mutuwa, babu mutuwa gidan Allah.
Babu yunwa, yunwa, babu yunwa gidan Allah.
Akwai jinƙai, jinƙai, akwai jinƙai gidan Allah.
Akwai rahama, rahama, akwai rahama gidan Allah.
Akwai ni’ima, ni’ima, akwai ni’ima gidan Allah.
Akwai waƙa, waƙa, akwai waƙa gidan Allah.
Akwai wahala, wahala, akwai wahala gidan Shaiɗan.
Akwai kuka, kuka, akwai kuka gidan Shaiɗan
Akwai daɗi daɗi, akwai daɗi gidan Allah.
LaIle jama’a, kan jama’a, lalle jama’a gidan Allah.
