Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 514 Sanadin Ceto, Yesu Ne Shi Lyrics
1
Sanadin ceto, Yesu ne shi,
Allah ya sa Yesu haka, in ji
Da farin soma wa’azin nan
Kofar alheri babu sai Ɗan.
KORUS
Shaidata wanna gaskiya ce:
Sani na yi, ni cetacce ne;
Fahariya babu, ni fansasshe,
Sani na yi, ni cetacce ne.
2
Zaman na ɗaure zamana dā,
Wyua, wahala, su duk na ke sha.
Tun da maganar Allah na ƙi,
Iblis, makiyinsa, na ke bi.
Korus
3
Ku masu ji, ku dakata dai,
Sai kun ji shaidata wannan sosai,
Yesu ya sayo ni, ya maida ni ɗa,
Babu mai raba mu har abada.
Korus
