Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 513 Sai Ku Tashi Dai Mutane Duk Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 513 Sai Ku Tashi Dai Mutane Duk Lyrics

 

1
Sai ku tashi dai mutane duk
Ku ji labarin mu
La…barin mayaki na Mai Ceto
Idan za ka ci nasara
Cikin yaƙin nan sosai
Sai ka nuna bangaskiya da aminci.

KORUS
Mayaƙi….na Yesu Kristi
Sai ka nuna halin kirki
Sai ka dogara gareshi
Ubangiji za shi bada nasara.

2
Duk maganar Ubangijinmu
A buɗe ta ke kuwa
Bari dai mu yi biyayya ba shakka
Ko Shaiɗan ya jarrabce mu
Ga mu nan da takobi
Sai mu ci gaba da ƙarfin zuciya.
Korus

3
A cikin yaƙin nan gaban mu
Mu yi tsayayya kuwa
Shaiɗan dai zai guje mamu nan da nan
Mu taimaki ƴanuwanmu
Mu yi shaida fa
Har ya zo ya kai mu gidan sama a can.
Korus

Exit mobile version