Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 51 Ya Allah, Ubangijina,Ka Ji Addu’ata Lyrics
1
Ya Allah, Ubangijina, ka ji addu’ata,
Bukatata mai yawa ce, kai ne mai bayarwa.
2
Ka sake mini zuciya, ka wanke ni. sosai.
Ka cika ni da Ruhunka, halinka na ke so.
3
Ka cika ni da ladabi, duk da bangaskiya.
Ka zauna kuwa a wurina, in zama gidanka.
4
In dinga tunawa da kai, kullum, ba fasawa.
Har muddar rai, har abada, Yesu Masoyina.