Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 509 Sabon Rai Kowa Lyrics
1
Yesu ya zo, ya kawo ceto
Yaba mu sabon rai,
Rai, sabon rai, rai domin kowa,
Yesu ya kawo rai.
KORUS
Ga sabon rai. Rai domin kowa,
Rai, sabon rai, mu yi murna da sowa
Yesu ya mutu domin dukanmu
Yesu ya kawo sabon rai.
2
Mu tashi dai duk, mu bada labari,
Labari na sabon rai
Kowa ya ji, kowa ya sani.
Yesu ya kawo rai.
Korus
3
Ya zubda jininsa
A bisa giciye
Domin ya saye zuciyarku
Ta koma wurinsa.
Korus
4
Bari ku ji, bari ku sani.
Yesu ya mutu
Domin dukarmu
Ya tashi don mu.
Korus
