Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 508 Sa’annan Matuƙa Za Ta Zo Lyrics
1
Wannan bishara kuwa ta mulki
Za’ayi wa’azinta ga duniya.
Domin shaida ga dukan al’ummai
Sa’annan mutuƙa za ta zo.
KORUS
Sa’annan, sa’annan, matuƙa, matuƙa
Sa’annan matuƙa za ta zo.
2
Gama kamar walƙiya daga gabas
Kuna ganinta kuwa bar yamma.
Haka nan Ɗan mutum za ya zo.
Sa’annan mutuƙa za ta zo.
Korus
3
Daga itacen ɓaure ku ga ne
Sai ku koyi misalinsa
Sa’anda yana hudo ganyensa
Sa’annan mutuƙa za ta zo.
Korus
4
Ku tuna da zamanin Nuhu ƴan’uwa
Ya sha ba’a cikin aikinsa
Amma ya ci gaba da yin jirginsa
Sa’annan matuƙarsu ta zo.
Korus
5
Sai mu jimre da aikin bishara
Har dukan duniya ta tsira
Domin Yesunmu yana zuwa
Sa’annan matuƙa za ta zo.
Korus
6
Yesu zai karɓe mu cikin sama.
Cikin gidan Ubansa.
Rawanin Rai yana jiranmu.
Sa’annan matuƙa za ta zo.