Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 507 Ranar Ubangiji Lyrics
1
Ranar Ubangiji fa tana zuwa babu shakka.
Al’umma duniya za su rushe
Masu aikata mugunta ranar su tana zuwa
Kamin ranar nan ka cece ni.
KORUS
I, gani nan Yesu na zo.
Ina neman ceto
Ka ji tausayi ka cece ni
Yesu gani ka cece ni.
2
Za mu ji ƙarar ƙafo daga can samaniya
Mai cetonmu yana sabkowa
Tare da mala’iku za su ware masu bi
Kamin ranar nan ka ceci ni.
Korus
(Karatu : I Tas 4 : 15-16
3
Masu bi da sun mutu daga ikon duniya
Za su fara jin ƙarar ƙafo
Waɗanda suke da rai daga nan za su tashi
Kamin ranar nan ka ceci ni.
Korus
4
Rana za ta yi dufu, taurare na faɗuwa
Samaniya tana sabkowa
Wata za ya ki bada haske babu sauren salama
Kamin ranar nan ka ceci ni.
Korus