Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 505 Oh Duniya Lyrics
KORUS
Oh duniya, oh duniya, runfar kara take fa.
Oh duniya, oh duniya, duniya mai shuɗewa.
1
Zaman duniya, zaman duniya, duniya sai iyawa.
Ka jingina ga duniya, sai ƙarewa za ta yi.
Korus
2
Ga masu bi na shan daɗi, sun manta da Allahnsu.
Ba addu’a, ba wa’azi, ai Shaiɗan ya ɗaure su.
Korus
3
Ga masu bi da arziki, sun maida shi Allahnsu.
Ga masu bi sun sami illimi, sun maida shi Allahnsu.
Korus
4
Ga masu bi, sun sami girma, sun maida shi Allahnsu.
Ba addu’a ba wa’azi, ai Shaiɗan ya ɗaure su.
Korus
5
Mu masu bi mu lura fa, ranan nan na zuwa fa.
Mu farfaɗo mu yi addu’a, biyayya ce za mu yi.
Korus
6
Kuɗi, girma, yabo, daɗi, ba za su cece mu ba.
Nemi Allah ba shi girma, shi fa zai bada ceto.
Korus