Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 50 Yesu Mai Jinƙai, Ubangijinmu Lyrics
1
Yesu mai jinƙai, Ubangijinmu,
Muna roƙonka, ba mu taimako.
Ya dutsen ceto, mafakarmu kuwa,
Yanzu ka ƃoye mu a cikinka.
2
Ba kuwa abu mai raba ni da kai.
Inda ka kai ni sai in riƙa bi.
Ba zan ji tsoron kome ba daɗai,
Gama Mai Ceto yana nan lalle.
3
Kai ne mai jinƙai, kai mai tausayi ne,
Kai ne mai ikon ka da zunubi.
Ni marar iko ne, ban iya ba,
Sai da ka zo ka zauna wurina.
4
Kome ƙoƙari, ni ban isa ba.
Shaiɗan ya jawo ni, shi ke da nasara.
Amma, ya Yesu, kai mafifici,
Ka zo gare ni har ka kore shi,
