Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 5 Halleluya, Halleluya, Halleluya, Ya Yesu Lyrics
Halleluya, Halleluya, Halleluya.
1
Ya Yesu, muna yabonka,
Mun taru don mu girmama ka,
Mu yi sujada gabanka. Halleluya!
2
Ya Kalmar Allah, Shaidarsa,
Bayani ne na darajarsa,
Haskaka mu har abada. Halleluya!
3
Ka gyarta mini zuciyata
Ka sa yabo a bakina,
Domin in yi ta ɗaukaka ka. Halleluya !
4
Ban da kai, raina wofi ne,
Aikina kuma banza ne,
Daɗi sai wurinka kaɗai. Halleluya!
5
Annabi, manzo, malami,
Mai ta’ aziyya, adili,
Yabo gare ka mu ke yi. Halleluya!
6
Yaushe zan duba fuskarka?
Yaushe ma zan ji muryarka?
Sai ran da ka karƃe ni can. Halleluya!